June 1, 2023

Amfani da man sauya fata na janyo cutar daji – NAFDAC

Hukumar da ke kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya, NAFDAC ta koka akan yaduwar mayukan da ke sauya launin fata a kasuwannin ƙasar, wadanda ta kira masu hadarin gaske.

Hukumar ta yi gargadin ne ranar laraba a wajen wani taron kara kwazon ma’aikata na kwana daya da aka shirya ma kafafen watsa labarai a jihar Enugu, mai taken, ‘hadarin da ke tattare da mayukan sauya launin fatar jikin dan adam da hanyoyin magance hakan.’

Da take jawabi a wajen taron, daraktar NAFDAC ta ƙasa, Farfesa Majisola Adeyeye wadda daraktan sashen kula da sinadarai da bincike na hukumar, Dr. Patrick Omokpariola ya wakilta ta ce, ya zama wajibi gareni in garagdi jama’a akan hadarin mayukan da ke sauya launin fatar jikin dan adam wadanda suka hada da cutar daji (Cancer), lalata muhimman sassan jikin dan adam, kona fatar jiki da janyo kuraje da tamoji da sa jiki tsufa da wuri tare da sa rauni ya dade bai warke ba.

Adeyeye ta bukaci matan Nijeriya da su zamo masu alfahari da kalar fatar jikin su, tare da cewa babu buƙatar su sauya launin fatar jikin su.

Ta kara da cewa, binciken hukumar lafiya ta duniya, WHO a shekarar 2018 ya nuna cewa kashi 77 na matan Nijeriya na amfani da man sauya fatar jiki, wanda shine mafi yawa a nahiyar Afirka idan aka kwatanta da kashi 59 da ƙasar Togo ke da shi da kashi 35 a Afirka ta Kudu sai kashi 27 na matan Senegal.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *